• Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bukaci gwamnatin tarayya ta yiwa matasan da aka kama lokacin zanga-zanga adalci
  • A taron da suka yi ranar Jumu'a a Taraba, gwamnonin sun yaba da yadda jihohi suka yi kokarin shawo kan masu zanga-zangar yunwa
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taronsu a Jalingo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Taraba - Gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko a inuwa jam'iyyar PDP sun gudanar da taro a jihar Taraba ranar Jumu'a.

A taron, gwamnonin ƙarƙashin inuwar kungiyar gwamnonin PDP sun tattauna batutuwa da dama ciki har da batun waɗanda aka kama lokacin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, kotun koli ta yanke hukunci kan sahihancin zaɓen gwamnan APC

Gwamnonin PDP sun aikawa Tinubu saƙo

Channels tv ta tattaro cewa bayan taron, ƙungiyar gwamnonin ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta tabbata an yiwa ƴan zanga-zangar da aka kama adalci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP sun kuma bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da waɗanda aka kama yayin zanga-zangar a gaban kotu kuma a yi masu adalci.

Hakan na kunshe ne a jawabin da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya yi bayan fitowa daga taron a Taraba.

Gwamnonin sun ƙara nanata ƴancin ƴan ƙasa na yin zanga-zangar lumana kana suka miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan masu zanga-zangar da aka kashe.

Abubuwan da gwamnonin PDP suka tattauna

Leadership ta ce a jawabin da ya yi, Gwamna Bala Mohammed ya ce:

"Wannan taro ya maida hankali kan batutuwan da suka shafi PDP da jihohin da take mulki da kuma wasu muhimman batutuwa da suka ja hankali a ƙasa.

Kara karanta wannan

Jigawa: masu zanga zanga sun kewaye gidan gwamnati, sun faɗi buƙatarsu

"Gwamnoni sun duba yadda aka ƙarƙare zanga-zaɓgar adawa da tsadar rayuwa, wacce ta kusa jefa ƙasar nan cikin rikici."Mun jinjinawa gwamnoni musamman na PDP bisa yadda suka magance lamarin cikin ƙwarewa, suka daƙile yunƙurin ɓata-gari na karɓe ragamar zanga-zangar."

PDP na maraba da kiran dawowar Jonathan

Kuna da labarin jam'iyyar PDP ta ƙasa ta nuna a shirye take ta marawa Goodluck Jonathan baya idan ya amince zai dawo a babban zaɓen 2027

Mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP, Ibrahim Abdullahi ya ce dama ba a yi wa tsohon shugaban ƙasar adalci ba a sukar da aka masa kan tsaro.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoNyfI9tbmajpWLBoq7BmquaZamexKJ5zJqqrmWqlruorYyzmKefkWKupa3LnKBmn6eWuq%2B7zaKlZqiUpXqorYyfnmg%3D